Asakir Radio
Asakir Radio

Matsala ta Lalacewa da tabarbarewar tarbiya da ake samu, zaka ga talaka ya mutu yabar marayu mutane sun yi watsi da dasu, tarbiyar su ko hidamar yau da goben su, bamai tuntuba ya suke rayuwa, Yawancin yaran da suke addabar al'ummah ku masu sara suka da shaye shaye 90% dinsu marayune iyayensu sun rasu, yan uwansu da makota sukai watsi dasu, karshe sai a wayi gari sun addabi kowa sakamakon wancan sakacin ne na rashin taimakeke niya tsakanin mutane.

Al'ummar mu ta kwayuka da rugage zakaga iyaye da kakanne musulmai ne Amma ko kalmar shahada basu iya ba anbarsu cikinjahilci, a wannan kuma 80% din masu fashi da makami a hanyoyi da dajijjika da masu satar mutane don a basu kudin fansa duk sune, kaji sunayen su na musulmai Amma basu san komai ba a musulincin, wannan ma hakki ne akan al'umma su bisu garuruwan su a koyar dasu addini. Haka kuma mugwayen aqidu ke ribatar wadannan mutane wajen tura su cikin halaka ta hanyar nuna musu miyagun aqidu.

Abokan zaman mu a kasashen mu wadanda ba musulmai ba, suma suna da haqqi kanmu wajen yi musu da'awa da kowanne salo , basu tallafi na kudi, gina musu wasu abubuwan more rayuwa da sauran dabaru na isar da addini.

Assahabatul Kiram

Assahabatul Kiram

Visit our website to get notified latest news and updates.

Visit our website

Follow us

Let’s follow our station on social media!

Follow on FacebookFollow on TwitterFollow on Youtube

Announcements

Ramadan Tafseer

Tafseer 2023 a Kaduna

March 8, 2023