
About
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya nazarci yadda aka yi fafatawa mai cike da armashi tsakanin Barcelona da Real Madrid wato haɗuwar hamayya tsakanin manyan ƙungiyoyin na Spain guda 2 karawar da ake kira El-Classico.
Yayin haɗuwar ta wannan karo dai, Real Madrid ce ta yi nasara da ƙwallaye 2 da 1 duk da ya ke wasan ya gudana ne a gidanta wato filinta na Santiago.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.