About
Shirin a wannan mako ya yi duba ne kan yadda ƴan wasan da ke taka leda ke dawowa gida don buga wasannin sada zumunci a lokacin da suke hutu.
A duk lokacin da aka kammala wasannin lig-lig a kan tafi hutu a kowace shekara musamman a nahiyar Turai da lig ɗin su ya fi jan hankali, wanda hakan kuma ke buɗe wani babi na wasanni a yankuna daban-daban da ƴan wasan ke fitowa domin nuna bajintarsu a zahiri a wasannin sada zumunta da a ke shirya musu.
Latsa alamar sauti don sauraren shirin...