
Shirin "Duniyar Wasanni" tare da Khamis Saleh a wannan lokaci zayyi duba ne kan ƙyautar gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafan Afirka da Achraf Hakimi na Morocco ya lashe.
A makon daya gabata ne Hukumar Kwallon Ƙafar Afrika CAF, ta bayar da kyautuka ga zaratan ƴan wasan nahiyar da suka nuna bajinta a wannan shekarar da muke bankwana da ita.
A yayin bikin da ya gudana a birnin Rabat na ƙasar Morocco, hukumar ta CAF ta sanar da ɗan wasan baya na tawagar ƙasar ta Morocco wanda kuma ya ke yi wa ƙungiyar PSG wasa Achraf Hakimi, a matsayin wanda ya lashe ƙyautar gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Afirka a wannan shekarar.
Hakimi ya samu nasarar ce bayan doke shahararrun ƴan wasan nahiyar da suka taɓa lashe kyautar irinsu Mohamed Salah na Masar da ke taka leda a Liverpool, da kuma Victor Osimhen na Nigeria da ke wasa a Galatasaray.
Wannan ne dai karo na farko da ɗan wasan ya taɓa lashe ƙyautar, bayan da a karo biyu a jere ya na ƙarewa a mataki na biyu, a shekarar 2023 da Victor Osimhen ya lashe da kuma 2024 da Ademola Lookman ya lashe.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...