
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan gasar lashe kofin duniya da za a fara a wannan makon. Ita dai wannan gasa ta lashe kofin duniya da aka faro a shekarar 1930, Hukumar Kwallon Ƙafa ta Duniya FIFA ce ke shiryata duk bayan shekara 4, sai dai a shekarun 1942 da kuma 1946 an samu tsaikon gudanar da gasar sakamakin yaƙin duniya na biyu.
Bayan kammala gasar da ƙasar Qatar ta karɓi baƙunci a shekarar 2022, jumullar ƙsashe 80 ne suka taɓa fafatawa a cikinta, inda aka buga wasan ƙarshe har 22 sai kuma ƙasashe 8 ne kawai suka taɓa lashe ta, inda Brazil ke da 5, Argentina da ke rike da kofin na da 4, Jamus da Italiya na da 3-3 sai Faransa da Uruguay da ta fara karɓar baƙuncin gasar ke da 2-2, yayinda Ingila da Spain kowaccensu ta lashe so guda-guda.
Ku latsa alamar sauti don sauaron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.............