
About
Shirin awannan mako ya leƙa gasar Firirmiyar Najeriya ne wadda ke gab da ƙarƙarewa, amma kuma haryanzu ba a san maci tuwon ba.
Yanzu haka dai an kammala wasannin mako na 35 a gasar Firimiyar Najeriya, wadda ya rage mako 3 kacal a kammala gasar a kakar wasa ta bana, amma sai dai haryanzu ƴar manuniya bata nuna ƙungiyar da za ɗauki gasar ba tsakanin ta saman teburi harzuwa wadda take a mataki na huɗu, saboda gajeruwar tazarar da ke tsakani, haka kuma abun yake a matakin ƙasan tebur inda nan ma ƙungiyar Wikki ce kadai kawo yanzu ake ganin da wahala ta tsallake, ya yinda ƙungiyoyin da ke mataki na 11 har zuwa matakin 19 kowaccen su bata da tabbas.