Skip to content
Opens in a new window
Nasarar tawagar ƙwallon ƙafar mata ta Najeriya akan Comoros
19 October 2026

Nasarar tawagar ƙwallon ƙafar mata ta Najeriya akan Comoros

Wasanni

About

Shirin 'Duniya Wasanni' a wanan mako tare da Khamis Saleh zai dubu ne kan nasarar da tawagar Super Falcons ta samu kan Comoros, inda a makon da ya gabata ne aka kammala wasa na biyu na zagaye na biyu na neman zuwa gasar Olympics da aka yi tsakanin tawagar mata ta Super Falcons ta Najeriya da takwararta ta Coromos.

An dai buga dukkanin wasanni biyu ne a filin wasa na Remon Star da ke garin Ikenne na jihar Ogun, inda a wasan farko Super Falcons ta samu nasara da ci 2 da nemam sannan a wasa na biyu aka tashi 5 da nema, a jumlace gida da waje Najeriya ta jefa kwallaye biyar da nema a ragar Comoros.