
About
Shirin a wannan lokaci zayyi duba ne kan yadda irin rawar da ƙasashen Afrika suka taka a wasannin rukuni a gasar lashe kofin duniya.
A ƙarshen mako ne dai aka kammala wasanni rukuni, abinda ke nuna cewar an buga wasanni 72 daga cikin 104 da za a yi a wannan gasa.
Sakamakon waɗannan wasani da aka yi ya nuna cewar anyi waje da tawagogin ƙasashe 16 daga cikin 48 dake fafatawa a gasar, inda ƙasashe 32 suka yi saura.
Nahiyar Afrika da ke da wakilcin ƙasashe 10, 9 daga cikin su sun samu nasarar kaiwa wannan zagaye, waɗanda suka haɗa da Afrika ta kudu da Senegal da Morocco da Ghana Ivory Coast da DR Congo da Algeria da Masar da kuma Cape Varde, inda Tunisia ta yi adabo da gasar.