Ra'ayoyin Masu Sauraro kan janye yajin aikin Likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya
15 September 2025

Ra'ayoyin Masu Sauraro kan janye yajin aikin Likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

About

Shirin Ra'ayoyin Mai Sauraro na wannan Litinin tare da Nasiru Sani ya tattauna ne kan janye yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyar da ƙugiyar likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya ta sanar a ƙarshen mako, kwanaki bayan fara ta a ranar Juma'ar da ta gabata, inda ta ƙara wa'aɗin makwanni  biyu don a biya musu buƙatunsu.

Daga cikin buƙatun ƙungiyar da take nema gwamnati ta biya akwai abinda ya shafi albashi da alawus-alawus da kuma walwalar mambobinta.

Ku latsa alamar sauti domin sauraron ra'ayoyin wasu daga cikin masu sauraro da suka aikoma ta manhajarmu ta Whatsapp