
09 October 2025
Ra'ayoyin masu saurare kan zaɓen shugaban ƙasar Kamaru
Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
About
A ƙasar Kamaru, yanzu haka ana ci gaba da yaƙin neman zaɓen shugabancin ƙasar da za a yi ranar lahadi mai zuwa, inda ƴan takarar 9 za su fafata da shugaba mai-ci wato Paul Biya.
Kawo yanzu dai yaƙin neman zaɓen na gudana a cikin kwancin hankali, yayin da tuni mahukunta suka yi gargaɗi domin kauce wa duk wani abu da zai iya haifar da matsala a wannan marra.
Shi me za ku ce a game da wannan zaɓe da ake shirin gudanarwar a Kamaru?
Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai.
Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...