Ra'ayoyin masu saurare kan taron manyan hafsoshin tsaron Afrika
27 August 2025

Ra'ayoyin masu saurare kan taron manyan hafsoshin tsaron Afrika

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

About

Hafsoshin tsaro na ƙasashen Afirka a taron da suka yi a birinin Abujan Najeriya, sun ƙuduri aniyar haɗa gwiwa don tunkarar ƙalubalen tsaro da nahiyar ke fuskanta.

Wannan taro dai ya samu halartar wakilan ƙasashe sama da 50, waɗanda suka yi imani da cewa la’akari da girman matsalar, akwai buƙatar ƙasashen su yi aiki a tare don tunkarar ta.

Shin ko meye ra’ayoyinku a game da wannan yunƙuri na ƙasashen Afirka?

Waɗannan shawarwari za ku bayar domin samun nasarar wannan fata?

Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai.

Latsa alamar sauti domin sauraren shirin....