
About
A jiya ne aka gudanar da bikin ranar malamai ta duniya cikin yanayin ƙuncin rayuwa da ƙarancin albashi, musamman a wasu ƙasashen Afirka da malaman ke ɗanɗana kuɗarsu.
An ware wannan rana ne, domin nuna goyon baya ga irin gudunmawar da suke bayarwa ga ci gaban rayuwar al’umma a fannoni da dama.
Wanne hali malamai ke ciki a yankunanku?
Shin kun gamsu da irin gudunmawar da suke bayarwa a yankunanku.
Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren shirin...