
11 September 2025
Ra'ayoyin masu saurare kan matakin Najeriya na haramta zirga-zirgar jiragen ruwa marasa lasisi
Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
About
A yunƙurin rage yawaitar haɗura akan ruwa, Hukumar Kula da Zirga-zirga a kan Kogunan Najeriya ta haramta yin amfani da jiragen ruwa a kan kogunan ƙasar sai tare da samun izini daga gare ta.
Wasu daga cikin matakan da hukumar ta sanar sun haɗa da hana yin lodin fasinja sai a tashoshin da ta amince da su, sai tilasta wa fasinja yin amfani da rigar kariya, da mallakar takardar shaidar ƙwarewa ga illahirin matuƙan jiragen da dai sauransu.
Anya waɗannan matakai za su taimaka don rage afkuwar haɗurra a kan kogunan Najeriya?
Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nasiru Sani.