
03 September 2025
Ra'ayoyin masu saurare kan kama Simon Ekpa mai fafutukar kafa ƙasar Biafra
Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
About
Kotun ƙasar Finland ta ɗaure Simon Ekpa mai fafutukar kafa ballewar Biafra daga Najeriya shekaru 6 a gidan yari, saboda samun sa da laifufukan ta’addanci.
Wannan hukunci na zuwa ne a daidai lokacin ake ci gaba da tsare ɗaruruwan mutane a gidajen yarin Najeriya bisa zargin aikata ta’addanci, amma kotuna sun gaza hukuntar da su.
Shin ko me za ku ce a game da wannan hukunci da kotun ƙasar Finland ta yanke?
Meye ra’ayoyinku a game da gazawar kotunan Najeriya wajen hukunta waɗanda ake tuhuma da aikata irin waɗannan laifuka a cikin gida?
Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu