Ra'ayoyin masu saurare kan ficewar ƙasashen AES daga kotun ICC
24 September 2025

Ra'ayoyin masu saurare kan ficewar ƙasashen AES daga kotun ICC

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

About

Burkina Faso, Mali da kuma Nijar sun sanar da janyewa daga Kotun Hukunta Laifuka ta Duniya da ke birnin Hague, bisa zargin kotun da kasancewa ƴar amshin ƴan mulkin mallaka.

To sai dai wasu na ganin cewa shugabannin ƙasashen uku sun ɗauki matakin ne don kauce wa bincike ko tuhuma daga wannan kotu.

Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacinku a yau cikin shirin na Ra'ayoyinku masu saurare.

Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...