Tarihin kafuwar Ƙungiyar Kare Hakkin Ɗan Adam ta Duniya
28 February 2026

Tarihin kafuwar Ƙungiyar Kare Hakkin Ɗan Adam ta Duniya

Tambaya da Amsa

About

A cikin shirin Tambaya da Amsa daga sashen hausa na RFI,a yau shirin ya mayar da hankali ne kan tarihin kafuwar Ƙungiyar Kare Hakkin Ɗan Adam ta Duniya ta Human Rights Watch, wanda ya samo asali daga ƙoƙarin sa-ido kan yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa, musamman a lokacin yaƙin cacar baka.

Hedikwatar ƙungiyar tana birnin New York na Amurka. Babban burinta shi ne bincike, tattara bayanai, da wallafa rahotanni kan take haƙƙin ɗan adam a faɗin duniya don matsa wa gwamnatoci lamba su gyara.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Nasiru sani.