
About
Send us a text
Wata cuta mai cin naman jikin dan’Adam ta yi sandin mutuwar mutum takwas yayin da wasu fiye da 60 suke kwance a asibiti a garin Malabu dake Karamar Hukumar Fufure ta Jihar Adamawa.
Wannan lamari dai ya jefa fargaba a zukatan mazauna yankin.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi bincike a kan yadda wannan cuta take yaduwa da matakan da ya kamata a dauka don kauce wa kamuwa da ita.