
About
Send us a text
A kwanakin nan ana samun raguwar kujerun maniyyata aikin Hajji daga Najeriya, abin da ya jawo fargaba ga masu shirin zuwa kasa mai tsarki da kuma masu hidimar su.
A da, Najeriya na samun kujeru sama da dubu casa’in daga gwamnatin Saudiyya, amma cikin shekaru kadan da suka gabata adadin ya ragu zuwa kusan dubu sittin da biyar.
Kazalika a yanzu gwamnatin na saudiyya ta bayyana cewa idan har maniyyatan Najeriya basu biya cikakken kudaden hajjin bana ba kafin wa'adin da suka gindaya, to akwai alamun sake rage yawan kujerun zuwa dubu hamsin.
Ko yaya kara raguwar kujerun maniyyatan Najeriya ke kara tasiri ga Najeriya?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin zai yi duba a kai.