Tasirin Takaddamar NUPENG Da Dangote A Kan Tattalin Arzikin Najeriya
09 September 2025

Tasirin Takaddamar NUPENG Da Dangote A Kan Tattalin Arzikin Najeriya

Najeriya a Yau

About

Send us a text

’Yan Najeriya sun shiga taraddadin abin da ka iya biyo bayana kudurin Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (NPENG) na tsunduma yajin aiki.


Hakan dai ya biyo bayan tashi da aka yi daga zaman da Gwamnatin Tarayya ta kira don sasanta kungiyar, mai samun goyon bayan sauran kungiyoyin kwadago, da rukunin kamfanonin Dangote, ba tare da cimma wata matsaya ba.


Ministan Kwadago Muhammadu Dingyadi ne dai ya kira taron, wanda ya samu halartar jami’an gwamnati da wakilan kungiyoyin NUPENG da NLC da TUC da na Dangote da kuma MRS, da nufin hana yajin aikin.