Me Dawowar Hare-hare Kan Sojoji Ke Nufi A Arewa Maso Gabas?
24 October 2025

Me Dawowar Hare-hare Kan Sojoji Ke Nufi A Arewa Maso Gabas?

Najeriya a Yau

About

Send us a text

A cikin ‘yan watannin da suka gabata, an sake ganin karuwar hare-haren Boko Haram da ISWAP musamman a yankin Arewa maso Gabas. Kazalika, ko a kwanan nan ma anga irin wadannan hare hare.


Wadannan hare-haren sun fi karkata kan sansanonin sojoji, inda ake samun asarar rayuka da dama, da kuma lalata kayan aikin gwamnati.

Rahotanni daga Borno da Yobe da ma wasu sassan kasar nan sun nuna yadda ‘yan ta’adda suka sake samun karfi wajen kai hare-hare cikin dare, tare da amfani da dabaru irin na soji da kuma kayan yaki na zamani. Wannan lamari ya jawo tambaya daga al’umma: shin wannan karin hare-hare alama ce ta dawowar kungiyar Boko Haram da ISWAP ne, ko kuma rashin isassun kayan aiki da dabarun soji ne ke jawo hakan?


Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.