Hanyoyin Magance Gubar Cikin Abinci
26 September 2025

Hanyoyin Magance Gubar Cikin Abinci

Najeriya a Yau

About

Send us a text

Cin guba ta hanyar abinci (food poisoning) wata cuta ce da ke faruwa idan mutum ya ci abinci ko ya sha abin sha da ya gurɓace. Gurɓacewar abincin na iya fitowa daga ƙwayoyin cuta kamar Salmonella, E. coli, ko Listeria, ko kuma daga ƙwayoyin cutar virus, ƙwari (parasites), ko sinadarai masu guba.


Alamomin cutar sun haɗa da ciwon ciki, amai, zazzabi, gudawa, da rashin jin daɗin jiki. A wasu lokuta masu tsanani, cutar na iya kai mutum asibiti ko ta yi barazana ga rayuwa, musamman ga yara ƙanana, mata masu ciki, tsofaffi, da masu raunin garkuwar jiki.


wannan shine batun da shirin Najeriya  A Yau na wannan lokaci zai yi duba akai.