
23 October 2025
Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Haraji Da Zai Fara Aiki A 2026
Najeriya a Yau
About
Send us a text
A ranar 26 ga watan Yuni, shekara ta 2025, gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan sabon tsarin haraji wanda za a fara aiwatarwa daga ranar 1 ga Janairu, 2026.
Wannan sabon tsarin haraji na daga cikin matakan da gwamnati ke cewa zai taimaka wajen kara samun kudaden shiga da kuma rage dogaro da albarkatun mai.
Sai dai, jama’a da dama ba su da cikakken bayani game da irin wadannan sabbin haraji ko menene suke nufi ba.
Shin ko ta wadanne hanyoyi ne wannan sabon haraji zai shafi rayuwar ‘yan Najeriya?