
Send us a text
A tsarin mulkin Najeriya, an bai wa Shugaban Ƙasa ikon naɗa shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) tare da sauran mambobinta. Wannan iko yana daga cikin muhimman nauyukan da ke hannun shugaban ƙasa domin tabbatar da cewa ana gudanar da zaɓe cikin tsari, gaskiya da adalci.
Sai dai, kafin wanda shugaban ƙasa ya naɗa ya fara aiki, dole ne a nemi amincewar Majalisar Dattawa, domin tabbatar da cewa wanda aka zaɓa ya cancanci rike wannan muhimmiyar kujera. Wannan tsari yana taimakawa wajen tabbatar da cewa hukumar zaɓe ta kasance mai zaman kanta, ba ta karkata ga wani ɓangare na siyasa ba, kuma tana iya gudanar da aikinta cikin gaskiya da amana.
wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.