Abin Da Doka Ya Ce Kan Kisan Jami’an ‘Yan Sanda
23 September 2025

Abin Da Doka Ya Ce Kan Kisan Jami’an ‘Yan Sanda

Najeriya a Yau

About

Send us a text

Kisan jami’an tsaro na cigaba da zama ruwan dare a Najeriya, lamarin da ya daɗe yana tayar da hankali, amma a ‘yan kwanakin nan abin ya ƙara muni.


Misali, kwanan nan a an kashe wasu jami’an ‘yan sanda a kananan hukumomin Katsina-Ala da Ukum a jihar Benue, inda ‘yan bindiga suka kai hari tare da kashe ‘yan sanda uku inda suka kuma sace wasu bakwai. 


Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan abin da dokokin kasa suka ce kan kisan jami'an 'yan sanda.