
Yaya Matsayar Katsalandar Din Da APC Tace Nyesom Wike Na Yi A Jam’iyyar?
Najeriya a Yau
Send us a text
A cikin ‘yan kwanakin nan, siyasar Najeriya ta sake daukar sabon salo, bayan barkewar takaddama tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, da manyan shugabannin jam’iyyar (APC). Jam’iyyar APC na kallon yadda Wike — wanda ba cikakken ɗan jam’iyyar ba ne amma ke rike da mukami a karkashin gwamnatinta — ke yin katsalandan a harkokin jam’iyyar, musamman a matakin jihohi, a matsayin barazana ga tsarin jam’iyya da ikonta na cikin gida.
Wannan lamari ya haifar da muhawara mai zafi a tsakanin ‘yan siyasa da masu sharhi kan harkokin siyasa.
Ko wanne matsaya jam’iyyar APC suka dauka kan wannan batu na katsalandan da Nyesom Wike ke yi a jam’iyyarsu?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.