
Send us a text
A ’yan shekarun nan, lokaci na bukukuwan ƙarshen shekara—wanda a da ake ɗauka a matsayin lokacin farin ciki, da haɗuwa da iyalai, da tafiye-tafiye—ya fara sauya salo ga mutane da dama. Maimakon shirye-shiryen ziyartar ’yan uwa ko halartar bukukuwa a garuruwa daban-daban, mutane da yawa yanzu suna cike da fargaba da damuwa. Babban dalilin hakan shi ne ƙalubalen tsaro da ke ƙara tsananta a sassa daban-daban.
Rahotanni na hare-haren ’yan bindiga, da sace-sace a kan manyan hanyoyi, da garkuwa da mutane, da rikice-rikicen da ke faruwa ba zato ba tsammani, sun sanya mutane da yawa sake tunani kafin su ɗauki hanya da sunan zuwa bukukuwan karshen shekara. Wannan yanayi ya sa wasu ke zaɓar zama a garuruwan da suke, wasu kuma suna rage nisan tafiya ko sauya tsare-tsaren bukukuwansu gaba ɗaya.
Ko yaya bukukuwan wannan shekarar za su kasance?
Wadanne matakai hukumomi ke dauka don kare lafiyan matafiya?
Wadannan da ma wasu tambayoyin shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi kokarin amsawa.