Sharuddan Da Jam'iyya Za Ta Cika Kafin Kiran Ta Babban Jam'iyyar Adawa
02 January 2026

Sharuddan Da Jam'iyya Za Ta Cika Kafin Kiran Ta Babban Jam'iyyar Adawa

Najeriya a Yau

About

Send us a text

A fagen siyasar Najeriya a halin yanzu, ana ta ce-ce-ku-ce kan wacce ce babbar jam’iyyar adawa da za ta iya tsayawa ƙafada da ƙafada da jam’iyyar APC mai mulki. Wannan takaddama ta fi karkata ne tsakanin jam’iyyar PDP, wacce ta dade tana taka rawa a matsayin babbar jam’iyyar adawa bayan ficewarta daga mulki a 2015, da kuma jam’iyyar ADC, wacce a ‘yan shekarun nan ta fara samun karɓuwa sakamakon shigar wasu manyan ‘yan siyasa da kuma ƙoƙarin gina sabuwar haɗaka a matsayin madadin tsoffin jam’iyyu.


Masu goyon bayan PDP na nuna cewa jam’iyyar na da tsari, da tarihi, da kuma gagarumar ƙafar da ta shimfiɗa a kusan dukkan jihohin ƙasar, lamarin da ke ba ta damar kiran kanta babbar jam’iyyar adawa. A ɓangaren guda kuma, magoya bayan ADC na jaddada cewa PDP ta raunana ne sakamakon rikice-rikicen cikin gida, da yawan sauya sheƙa, da gajiyar da al’umma ke nunawa ga tsoffin jam’iyyun siyasa.
Kazalika anga yadda manyan jiga-jigan siyasa keta dinkewa wuri daya a jam’iyyar ADC wanda ake ganin ta fara shafe jam’iyyar ta PDP a matsayin babban jam’iyyar adawa a Najeriya.
Ko me da me ake dubawa don gane babban jam’iyyar adawa a Najeriya?


Wannan shine batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba akai.