
Send us a text
A shekarar 2025, Najeriya ta fuskanci manyan ƙalubalen tsaro da suka fi daukar hankali, musamman hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane, da ta’addanci a jihohin Arewa kamar Zamfara, da Katsina da Sokoto da Kaduna da kuma Borno. Hare-haren sun yi sanadin rasa rayuka, da rufe makarantu, da kaura daga gidaje, da kuma durkushewar harkokin tattalin arziki a wasu yankuna.
Wadannan matsaloli suka sa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro, domin daukar matakan gaggawa na kare rayuka da dawo da doka da oda wanda hakan yasa shugaban kasa dawo da tsohon babban hafsan rundunar sojin Najeriya a matsayin ministan tsaro.
Shirin Najeriya a yau na wannan lokaci zai yi waiwaye ne kan manyan kalubalen tsaro da suka faru a 2025.