
27 September 2025
Yadda manoma a Jahuriyar Nijar suka koma noman Gyaɗa da Gujiya gadan-gadan
Muhallinka Rayuwarka
About
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda manoma a Nijar suka koma noman Gyaɗa da riɗi gadan-gadan bayan sun yi watsi da shi tsawon shekaru, saboda matsaloli da noman ke fuskanta.Maraɗi ce kan gaba a noma Gyada ko Gujiya shekaru aru aru, sai Zinder da kuma Doso, waɗanda suka taimaka wajan hada-hadar kasuwancin Gyaɗa har a Kano inda ake tattara Dalar Gyadar.Yawan noman Gyadar ne ma ya sa turawan mulkin mallaka suka kafa masana’antar sarrafa man Gyada a 1943 a Maraɗi.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson...........