
09 August 2025
Yadda jihar Yobe ke ƙoƙarin rage rashin ayyukan yi tsakanin matasa ta hanyar habbaka noma
Muhallinka Rayuwarka
About
Shirin ‘Muhalllinka Rayuwarka na wannan makon zai yaɗa zango ne a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda duba da cewa noma shi ne ginshikin tattalin arzikin jihar Yobe, inda kusan kashi 90% na al’ummar jihar ke harkar noma da kiwo.
Gwamnatin jihar ta kaddamar da mataki na biyu na rabon kayan aikin noma domin kara samar da abinci da karfafa tattalin arzikin cikin gida tare magance rashin ayyukan yi tsakanin matasa da zummar magance barazanar matsalolin tsaro da shigar matasa kungiyoyin ‘yan ta’adda.
Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Micheal Kuduson