Shirin gwamnatin Jigawa na farfado da noman yankin Sahara a jihar
19 July 2025

Shirin gwamnatin Jigawa na farfado da noman yankin Sahara a jihar

Muhallinka Rayuwarka

About

Tun a karshen watan Fabrairun wannan shekara da muke ciki, wato shekarar 2025, gwamnatin jihar Jigawa ta  kaddamar da shirin noman na yankin sahara karamar hukumar Maigatari dake masarautar Gumel.

A  jawabin da ya gabatar a yayin kaddamar da shirin, gwamnan jihar, Umar Namadi ya ce an kirkiro shirin ne don bunkasa noma da samar da abinci da ayyukan yi da kuma rage kwararar mutane daga kauye zuwa birane.