
About
Shirin Muhallinka Rayuwa na wannan mako yayi duba ne kan yadda ake ƙara samun ƙaruwar yin noman cikin gida musamman a yankin Arewacin Najeriya, yankin da hukumomi suka dade suna kiraye kiraye kan a rungumi harkar noman. Za mu kuma duba yadda hakan zai taimaka wa wadata ƙasa da abinci da kuma fa’idarsa ga muhalli.