Alfanun cibiyar bunƙasa noma a jihar Kano ga ci gaban samar da abinci a Najeriya
11 October 2025

Alfanun cibiyar bunƙasa noma a jihar Kano ga ci gaban samar da abinci a Najeriya

Muhallinka Rayuwarka

About

Shirin Muhallinka Rayuwarka tare da Michael Kuduson a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda aka samar da wata katafariyar cibiyar bunƙasa harkokin noman Damuna dana Rani ga al'ummar jihar Kano wadda aka samar a garin Kadawa da ke ƙaramar hukuamr Garin Malam.

bayanai sun ce wannan cibiyar bunƙasa noma na ƙunshe da tarin kayakin buƙata a lokacin noman walau na rani ko kuma na damuna duk dai a ƙoƙarin haɓaka harkar noma a jihar ta Arewa maso yammacin Najeriya.

Bankin Musulunci da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Kanon ne suka samar da wannan cibiya wadda ta laƙume biliyoyin dalolin Amurka ƙarƙashin shirin KSSB na haɓaka noma bisa kulawar SASAKAWA.

Ku latsa alamar tsari don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson.....