
14 April 2026
Dalilan da suka sanya Manoma Albasa a Nijar fuskantar ƙalubale a bana
Muhallinka Rayuwarka
About
Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' na wannan makon, ya yi tattaki zuwa Jamhuriyar Nijar, inda aka fuskanci ƙalubale kan noman Albasa a shekarar bana.
Bayanai daga ƙasar ta Nijar na cewa a halin da ake ciki, Manoma da dama sun shiga halin ƙaƙa-ni-kayi saboda rashin samun kuɗaɗen shiga, la'akari da irin rawar da noman na Albasa ke taka wa wajen sama musu abin kashewa.