
Shirin muhallinka rayuwarka na wannan makon ya tattauna ne kan yadda sauyin yanayi ko dai na zafi ko na sanyi ko kuma damina ke bayyana ƙarara, musamman a yankin yammacin Afirka. Ga misali a Najeriya, ɗaya daga cikin sauye-sauyen yanayin da aka shaida shi ne rashin hunturu a shekarar bana, musamman a Yankin arewacin ƙasar, inda aka saba ganin kankamar Yanayin na sanyin mai tsanani daga ƙarshen watan Nuwamba ko farkon Disamba zuwa ƙarshen watan Janairu ko farkon Fabarairu.
Gabanin fuskantar wannan lamari dai hatta yanayin damina da lokacin zuwanta ya sauya daga abinda aka saba da shi, batun da hatta a wasu wuraren da ke yankin Kudu maso yammacin Najeriya ma an shaida hakan.
Tuni dai wannan al’amari na sauyin lokutan yanayin zafi da damina ko kuma sanyi ya zama abin tattaunawa a tsakanin jama’a dangane da dalilan da suka janyo hakan, da dai wasu sauran tambayoyi da ake da ƙishirwar neman amsoshinsu.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare Nura Ado Suleiman............