Yadda manoman Jamhuriyar Nijar ke fama da ɓarnar makiyaya a ƙarshen damina
29 November 2025

Yadda manoman Jamhuriyar Nijar ke fama da ɓarnar makiyaya a ƙarshen damina

Muhallinka Rayuwarka

About

Shirin muhallinka rayuwarka na wannan karon zai mayar da hankali ne kan irin fama da ake sha a karshen damina tsakanin manoman da suke tattarar Kayan gona da makiyayan dake dawowa daga kiwo zuwa wuraren da ake aikin noman a  wasu sasaan Jamhuriyar Nijar.

A duk karshen damana makiyayan da suka tafi mashekari wurin kiwon dabbobinsu inda ke da isassar ciyawa nesa da gonaki na sabkowa wuraren da ake aikin noma don ganawa da jama'a, sannan da samun sauran tarikicen da manoman suka bari a gonakansu. Sai dai a irin lokacin na komawar makiyayan ana samun rikicin dake faruwa ' tsakaninsu da manoman da ba su ida tattare Kayan da suka noma ba, kuma da yanda wasu makiyayan ke saurin komowa a lokacin da manoman ke tsaka da aiki, duk da an tanadi dokar da ta tsaida komi a kasar ta Nijar.