
02 May 2026
Matsalar karancin tsaftataccen ruwa, na ci gaba da addabar iyalai a sassan Nigeria
Muhallinka Rayuwarka
About
Matsalar nan ta karancin tsaftataccen ruwa, na ci gaba da addabar miliyoyin iyalai a sassan Nigeria, kila ko saboda rashin samun damar jan ruwan famfo a gidajensu, ko kuma rashin samun ruwan daga hukumomin samar da ruwan famfo na jihohinsu, duk da makudan kudin da gwamnatocin jihohin ke warewa, da sunan samar da ruwa wa jama’arsu.
Wannan matsala ba kawai ta tsaya kan iyalai da kan rasa ruwan amfanin yau da kullum a gidajensu ba, har ma tana shafar ingancin muhalli, kasancewar a kan muhallin a kan dawo, don neman ruwan a karshe.