
12 July 2025
Yadda hare-haren ta'addanci ke ci gaba da sanadin mutuwar mutane a Najeriya
Mu Zagaya Duniya
About
Hukumar kare hakkin ɗan Adam ta Najeriya ta ce adadin mutanen da ‘yan ta’adda suka kashe a cikin watanni shidan farko na wannan shekara, ya zarce adadin da aka lissafa a shekarar bara.
Ƙungiyar direbobin motocin dakon kaya a Senegal ta koka kan matsalolin tsaro da suka fara shafar yankunan kan iyakar ƙasarsu da Mali, inda ta yi barazar dakatar zirga-zirga zuwa Malin muddin mahukunta suka gaza ɗaukar matakan da suka ɗace.
Kakakin majalisar dokokin Kenyan ya goyi bayan bai wa ‘yan sandan Umranin harbe duk mai zanga-zangar da aka samu yana satar dukiyar jama’a da lalata kayan gwammnati.
A Amurka kuwa Ambaliyar ce ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutane 119
Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman.