Tsaffin jami’an ƴansanda a Najeriya sun gudanar da kwarya-kwarayar zanga-zanga
26 July 2025

Tsaffin jami’an ƴansanda a Najeriya sun gudanar da kwarya-kwarayar zanga-zanga

Mu Zagaya Duniya

About

Masu saurare barkan mu da safiya Rukayya Abba Kabara ce ke farincikin kasancewa da ku a cikin sabon shirin Mu zagaya Duniya,a cikin shirin zaku ji yadda mutane sama da miliyan biyar ke fama da tsananin yunwa a wasu jihohin arewa maso gabashin Najeriya uku.

Wannan mako ne tsaffin jami’an ƴansanda a Najeriya suka gudanar da wata kwarya-kwarayar zanga-zanga a babban birnin tarayyar Abuja.