Trump ya ƙaƙaba sabbin takunkuman hana shiga Amurka
20 December 2025

Trump ya ƙaƙaba sabbin takunkuman hana shiga Amurka

Mu Zagaya Duniya

About

Mu Zagaya Duniya wanda ke bitar wasu daga cikin muhimman lamurran da suka wakana  a makon da muka yi wa bankwana,shirin zai fara ne da matakin da shugaba Donald Trump ya ɗauka na ƙaƙaba sabbin takunkuman hana shiga Amurka kan wasu ƙarin ƙasashe bakwai na Afrika, ciki har da Burkina Faso da Mali da kuma Jamhuriyar Nijar a bisa dalilan da ya  ce na tsaro ne.