
Trump ya jagoranci ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya
Mu Zagaya Duniya
Daga cikin labarun da shirin 'Mu zagaya Duniya' na wannan makon akwai yarjejeniyar zaman lafiyar da shugabannin ƙasashen yankin Gabas ta tsakiya suka ƙulla a ƙarƙashin jagrancin takwaransu na Amurka Donald Trump, sai kuma waiwayar halin da ayyukan agaji ke ciki a Zirin Gaza, bayan tsagaita wutar da aka yi tsakanin Isra’ila da Hamas.
A Najeriya kuwa shirin zai waiwayi taron da Malamn Addinin Musulunci suka yi a Kaduna kan yadda amfani da kafafen sadarwa na zamani ba bisa ka’ida ba gami da tattaunawa kan lamurran da suka shafi tsaro da tabarbarewar tattalin arziki. Sai kuma ziyarar da Ministan harkokin wajen Faransa Jean Noel Barrot ya kai ƙasar.
Muna kuma ɗauke da rahotanni kan lamurran da suka wakana a Kamaru cikin makon da muka yi wa adabo, inda ake ci gaba da dakon fitar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.
Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Nura Ado Suleiman.............