
About
A wannan mako shirin Mu Zagaya Duniya ya faro ne daga hare-haren da 'yan bindiga suka ƙaddamar a Najeriya, inda suka sace ɗalibai 25 a makarantar sakandiren Maga ta jihar Kebbi, da kuma harin da suka kai mujami'ar jihar Kwara, sai na Zamfara, da Sokoto, da Borno da kuma Neja.
Shirin ya kuma leƙa sauran ƙasashen Afrika da ma Nahiyar Turai, don yin bitar labaran da muka kawo muku a makon da muke bankwana da shi.
Latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Azima Bashir Aminu...