RFI Hausa ta cika shekaru 19 da fara watsa labarai cikin harsshen Hausa
23 May 2026

RFI Hausa ta cika shekaru 19 da fara watsa labarai cikin harsshen Hausa

Mu Zagaya Duniya

About

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' ya fara ne da labarin cikar wannan tasha ta RFI Hausa shekaru 19 da kafuwa. 

Ranar alhamis 21 ga wannan watan gidan Rediyonku na RFI sashen Hausa ya cika shekara daya- daya har 19 da soma yada shirye-shiryensa .

A shekara 2007 ne kwarrariyar ƴar Jarida Lanni Smith ta kirkiri sashen Hausa na RFI da aka yi wa matsuguni a birnin Lagos da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Kuma bikin na bana yazo a wani yanayi da kafar ke kara samun daukaka a idon duniya.