Najeriya ta tabbatar da harin da Amurka ta kai a wasu yankuna na jihar Sokoto
27 December 2025

Najeriya ta tabbatar da harin da Amurka ta kai a wasu yankuna na jihar Sokoto

Mu Zagaya Duniya

About

A cikin daren  ranar Alhamis da ta gabata Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da harin da Amurka ta kai a wasu yankuna biyu na jihar Sokoto wato Tangaza inda nan ne ‘yan Lakurawa ke da maɓoya da kuma Jabo da ke yankin ƙaramar hukumar Tambuwal.

Sai dai mazauna yankin Jabo sun bayyana fargabar zama a ƙauyukansu saboda fargabar yin kuskuren kai musu farmaki a yayin wasu hare-haren da watakila Amurkar ka iya kai wa a nan gaba.