
About
Daga cikin batutuwan da shirin ya waiwaya akwai taron da Manyan hafsoshin tsaron ƙasashen Afrika suka yi kan matsaloli musamman na ta’addanci da suka addabi nahiyar.
Sai shirin ƙungiyar ƙasashen ECOWAS na haɗa makekiyar rundunar haɗin gwiwa irinta ta farko, da za ta ƙunshi dakaru dubu 260,000
Akwai bitar rahoton binciken da ya gano ƙaruwar yawan attajirai a Nahiyar Afrika
Sai kuma zaman da kwamitin tsaron Majlisar Ɗinkin Duniya ya yi kan halin da ake ciki a Zirin Gaza, yankin da a Juma’ar nan da ta gabata Isra’ila ta dakatar da shigar da kayan abinci zuwa cikin babban birninsa.