
10 January 2026
Bitar muhimman labaran da suka gudana a makon da muke bankwana da shi
Mu Zagaya Duniya
About
A cikin shirin na wannan mako tare da Oumarou Sani, zakuji bitar muhimman labaran da suka wakana a makon da muke bakwana da shi, ciki har da yadda Amurka ta yi gaban kanta wajen kutsawa cikin Venezuela tare da kame shugaba Nicolas Maduro.
Muna tafe da tattaunawar masana a ɓangarori daban-daban kan wannan katsalandan na Amurka.
Hallau dai a cikin shirin zaku ji bitar ɓarkewar sabon rikici a Yemen da Syria.
A Najeriya kuwa akwai mu da bitar hare-haren ƴan ta'adda a jihar Neja da kuma rikicin siyasar ƙasar.
Ku latsa lamar sauti don sauraron cikakken shirin.