
16 August 2025
Bitar mako: Rundunar Sojin Najeriya ta samu nasarar kashe ‘yan ta’adda kusan 600
Mu Zagaya Duniya
About
Wasu daga cikin labarun makon da ya gabata da shirin 'Mu Zagaya Duniya' ya waiwaya a wannan karon sun haɗa da, nasarar da rundunar Sojin Najeriya ta samu na kashe ‘yan ta’adda kusan 600 da yarjejeniyar sayen makamai da ƙasar ta ƙulla da Amurka.
Sai kuma a fannin tattalin arziƙi, inda wata tawaga ta musamman daga ƙasar Qatar ta fara ziyarar makwanni kusan 3 a wasu ƙasashen nahiyar Afrika domin ƙulla yarjeniyoyi gami da zuba hannayen jarin biliyoyin Dalar Amurka a ƙasashen aƙalla 10.