Bitar Labaran Mako: Naɗin sabon ministan tsaron Najeriya Janar Christopher Musa
06 December 2025

Bitar Labaran Mako: Naɗin sabon ministan tsaron Najeriya Janar Christopher Musa

Mu Zagaya Duniya

About

Shirin Mu Zagaya Duniya tare da Azima Bashir a wannan mako ya yi bita tare da bibiyar manyan labarai mafiya jan hankali a makon da mukayi bankwana da shi daga sassa daban-daban na duniya.

Labarai mafiya jan hankali a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi shi ne naɗin sabon ministan tsaro Janar Christopher Musa mai ritaya bayan murabus ɗin bazata da Alhaji Badaru Abubakar ya yi daga kan kujerar bisa dalilai na rashin lafiya dai dai lokacin da matsalolin tsrao ke ci gaba da ta’azzara a wannan ƙasa.

Sai kuma batun tantance ƙarin Jakadun da shugaba Tinubu ya miƙawa Majalisar dattijai kana mutuwar ɗan adawa Anicet Ekane can a Kamaru, yayinda aka ga yadda tattaunawa ta yi nisa da fatan kawo ƙarshen yaƙin Ukraine tsakanin masu shiga tsakani, a gefe guda kuma aka ƙulla yarjejeniya mai cike da tarihi tsakanin Congo da Rwanda bisa jagorancin Amurka.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.