
18 April 2026
Bitar Labaran mako: Iran ta amince da buɗe mashigin Hormuz ga jiragen kasuwanci
Mu Zagaya Duniya
About
Shirin Mu zagaya duniya tare da Oumarou Sani, kamar yadda ya ke zuwar muku a kowannen mako, a wannan karon ma ya yi bita ne kan muhimman labaran da suka faru a makon da muke ban kwana da shi.
Cikin jerin labaran da ke ƙunshe a wannan shiri, akwai yadda Iran ta amince da buɗe mashigin Hormuz bayan ƙulla yarjejeniyar tsagaita wutar kwanaki 10 tsakanin Isra'ila da Lebanon.
Wannan da sauran manyan labarai daga sassa daban-daban na nan ƙunshe a cikin shirin.
Ku latsa alamar sauti don saurare.