
Ana ci gaba da laluben dubban mutanen da suka ɓata a girgizar kasa a Venezuela
Mu Zagaya Duniya
Shirin na wannan mako zai soma ne daga Venezuela inda a yammacin ranar laraba girgiza ƙasa mai karfin maki 7 a ma’aunin celcius ta afkawa arewa maso yammacin ƙasar abin da ya jefa al'umma cikin mawuyacin hali da alhini sakamakon rasa rayuka da dukiyoyi.
Alkaluman hukumomi sun ce sama da mutum 900 ne suka rasayukansu kawo yanzu yayin da sama da 4,000 suka jikkata bayaga sama da 50,000 da suka yi ɓatan dabo.
Tuni dai Ƙasashe suka fara aike da saƙonni jaje baya ga jami’an agaji don taimakawa a aikin laluben mutanen da girgizar ƙasa ta birne da kuma waɗanda ke cikin mawuyacin hali.
A nahiyar Turai kuwa matsanancin zafi ya tilasta dakatar da harakokin yau da kullum a ƙasashe da dama.
A wasu birane zafin ya kusa kai maki 40 a ma’aunin Celsuis abin da ya tilsatawa mahukunta fitar da gargaɗi da dakatar da muhimman harakokin yau da kullum.
A Faransa, an rufe ɗaruruwan makarantu a ranar Litinin yayin da aka rage lokacin tashin wasu dubbai.
A wani labarin kuma, ranar Alhamis da ta gabata al’ummar musulmi mabiya ɗarikar Shi’a a duniya suka gudanar da juyayin tunawa da kisan jikan Annabi Muhammad SAW, da aka yi a garin Karbala na ƙasar Iraqi ta yanzu, kwanakin da ke yiwa laƙabi da Tasu’a da Ashura.
A ƙasar Iran wadda itace cibiyar mabiya Shi’a a duniya an gudanar da bikin na wannan rana a cikin yaƙi da kuma rashin jagoran addinin ƙasar Ayatoullah Ali Khamna’ei, wanda ke jagorantar ranakun a kowacce shekara.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Oumarou Sani.